Zaben Shugabannin Jam’iyyar PDP a matakin Kananan Hukumomi da aka gudanar ranar Asabar a Jihar Sokoto ya bar baya da kura kamar yadda ‘yan takara da bangarori da dama suka yi korafin ba a yi masu adalci ba.
Rariya ta labarto cewar a bakidaya Kananan Hukumomi 23 an zabi ‘yan takarar ne a matakin sulhu ba tare da fafatawa a zabe kamar yadda Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya bayar da umurni domin samar da maslaha domin ganin ba a samu rarrabuwar kawuna ba.
Sai dai daya daga cikin ‘yan takarar a Karamar Hukumar Sakkwato ta Arewa, Alhaji Kasimu Ummarun Kwabo (Dangaladiman Jarma) ya bayyana cewar taron da aka gudanar a yau ba zabe ba ne, illa nadi ne kawai aka yi kuma ba da yawunsu aka yi ba.
Jaridu sun ruwaito sabanin da aka samu a wajen taron masu ruwa da tsakani na Jam’iyyar PDP a makon jiya tsakanin Gwamna Tambuwal da tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa wanda ya yi korafin rashin baiwa bangarensa muhimmanci a jam’iyyar wadda suka yi ruwa da tsakin kafawa a 2019.
A ta bakin Alhaji Kasimu Ummarun Kwabo daga Mazabar Magajin Gari (B) a zantawarsa da manema labarai ya ce sun je wajen zaben amma aka hana masu shiga saboda ba a ba su katin ratayawa na shiga ba. “Daga baya mun ji cewar ga wadanda aka zaba, amma kuma a iya sanin mu ba zabe aka gudanar ba, duk abin da aka yi ba da yawun mu aka yi shi ba. Tun farko mun kai korafin mu a wajen uwar jam’iyya da shugaban jam’iyya na Jiha da kwamitin gudanar da zaben amma ba abin da aka yi.” In ji shi.
Alhaji Bello Mai- Karfi da wasu mutane 18 ne aka aminta da su a matsayin wadanda za su jagoranci jam’iyyar a Karamar Hukumar Sokoto ta Arewa a taron wanda aka gudanar a babbar cibiyar taro da ke Kasarawa.
“Mai Girma Gwamna ya bayar da umurnin a je kowace Karamar Hukuma a zauna da kowane bangare a tsara yadda za a kasafta mukaman da yadda za a raba su, amma a hakikanin gaskiya a Sokoto ta Arewa ba haka aka yi ba domin sun sa kafa sun shure umurnin da Mai Girma Gwamna ya bayar.”
Ya ce “Tun da farko sai da suka kammala zaman su a Sakkwato ta Arewa sa’annan aka kira mu, sun zauna su kusan 40 zuwa 50 amma mu a namu bangaren mutum shida kawai aka kira, suka ce ga yadda suka tsara. Haka ma maimakon a turo mana ‘yan siyasa mu zauna da su sai aka turo mana ma’aikatan Gwamnati kamar Manyan Sakatarori da Manyan Daraktoci da Sakataren Karamar Hukuma da ire-iren su.”
Ya ce ko kadan ba adalci ba ne yadda aka hada mutane tara a daya bangaren su kuma a nasu bangaren su biyu kacal aka ce za a yi masu zabe bayan sun kasa sasanta kan su don haka a cewarsa sun bukaci a aiwatar da zaben da kowa zai aminta amma ba a yi ba.
Dan takarar Alhaji Kasimu Ummarun Kwabo ya bayyana cewar a zaben ba a siyarwa kowa fom ba a bisa ga bukatar Tambuwal ta samar da sulhu ba tare da wata hayaniya ba don haka ya bayar da umurnin a sasanta.
“Muna kira ga Mai Girma Gwamna a bisa ga adalcinsa ya shiga cikin lamarin nan, ya jagoranci gyara na tsakani da Allah domin harka ce ta siyasa, jama’a za a yi wa aiki don haka idan za a yi abu a yi shi yadda ya kamata domin samar da maslaha ga kowa.” Ya bayyana.