Rahotanni sun nuna cewa ‘yan bindiga sunyi Garkuwa da Wasu Almajirai da ba’a tantance adadinsu ba a Gidan Bakuso dake karamar hukumar Gada a jihar Sakkwato. An bayyana cewa an sace daliban ne daga makarantarsu da misalin karfe 1:00 na safiyar Yau Asabar.
Shugaban Makarantar, Liman Abubakar, ya shaidawa Wakilin KBC Hausa cewa a halin yanzu dalibai 15 ba a san inda suke ba, amma har yanzu ana kan kirgawa. Abubakar ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun mamaye garin ne da misalin karfe daya na safiyar Yau, inda suka harbe mutum daya sannan suka yi awon gaba da wata mata.
Suna fitowa daga garin sai suka hangi dalibanmu sun ruga cikin dakunansu, kuma sun yi garkuwa da yawa daga cikinsu. “Ya zuwa yanzu mun kirga mutane 15 da suka bata, kuma muna ci gaba da neman karin wasu,” inji shi. Abubakar ya kara da cewa ba wannan ne karon farko da ‘yan bindiga suka kai hari kauyen ba.