A cikin karshen makon da ya gabata ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari yankin Gobirawan Cali da ke karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara inda suka yi awon gaba da manoma 40.
Wani mazaunin kauyen ya sanar da BBC cewa ‘yan bindigan sun tsinkayi kauyen inda suka dinga harbe-harbe yayin da mazauna kauyen suka dinga gudu domin buya a daji.
Kamar yadda mazaunin kauyen yace, “Sun zo da tarin yawansu inda suka shiga yankin tare da fara harbe-harbe.
“Da yawanmu mun dinga gudu domin tsira. A halin yanzu babu jama’a a kauyen. Mun tsere daruruwanmu saboda sun yi mana zuwan ba-zata.”
Wurin karfe uku na yamma ‘yan bindiga sun shiga kauyen inda suka yi kokarin sace mutum daya wanda suka fafata dambe da daya daga cikin ‘yan bindigan inda ya maka shi da kasa tare da kwace bindigarsa kirar AK 47.
“Da gaggauwa ya dauke bindigar sannan ya wurga ta cikin wata gonar masara a kusa da shi. Dan bindigar ya farfado inda ya tsere ya shiga daji
“Bamu san cewa ‘yan uwansa suna kusa ba.
Daga nan sai suka fito da yawansu inda suka dinga harbe-harbe. Mun tsere amma sun sace manoma 40. Wasu dai a halin yanzu sun tsero.
“Mun yi kokarin kiran jami’an tsaro saboda babu sabis hakan mu bai cimma ruwa ba. A yanzu yankinmu babu kowa kuma ba za mu koma ba har sai gwamnati ta samar mana da tsaro.”