Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Sokoto: ‘Yan Bindiga Sun Kai Harin Ramuwar Gayya

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewar wasu gungun Yan bindiga sun kai sabon hari wani ƙauye a ƙaramar hukumar Tangaza, jihar Sokoto, inda suka hallaka mutum shida, da raunata wasu da dama.

Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun farmaki ƙauyen, wanda mafi yawancin mutanen cikinsa mafarauta ne, da sanyin safiyar ranar Lahadi. Kuma yan bindigan sun kai harin ne dai-dai lokacin da mafi yawan mazan garin sun fita sana’arsu ta farauta.

Sai dai babu tabbacin cewa ko harin miyagun yana da alaƙa da kashe yan bindiga 13 da mutane suka yi, waɗanda suka kai hari garin Tangaza ranar Asabar.

Wata majiya ta shaidawa Dailytrust cewa wasu mata biyu na cikin waɗanda miyagun maharan suka hallaka a lokacin harin. Yace: “Sun bindige mata guda biyu har Lahira, yayin da suka yanka matasa guda huɗu yayin mummunan harin.”

“Dukka yan bijilanti da kuma yan sa kai dake yankin sun bazama cikin daji domin neman waɗanda suka aikata wannan mummunan ta’addancin.”

A ranar Asabar, fusatattun mutane suka sheƙe tare da ƙone gawarwakin wasu yan bindiga 13, waɗanda suka kai hari garin Tangaza suka kashe mutum huɗu.

Exit mobile version