Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Sokoto: Uwargidan Gwamna Ta Samar Da Asibitin Yoyon Fitsari

Uwargidan Gwamnan Jahar Sokoto Hajiya Mariya Aminu Waziri ta samar da Asibitin Mata masu Yoyon Fitsari Irin na Zamani a birnin Sokoto

Gidauniyar MTDI tareda hadin gwiwar NFPA karkashin jagorancin uwar gidan gwamnan jahar sokoto Hajiya Maria Aminu Waziri Tambuwal ta gina sabuwar asibitin zamani ga mata masu fama da matsalar yoyon fitsari.

Uwar gidan gwamnan ta bayyana cewa babban dalilin da yasa akayi wannann asibiti shine domin taimakawa mata masu fama da yoyon fitsari, musamman matan karkara wadanda suka kasance basu ciki zuwa awon ciki ko kuma haihuwa a asibitoci ba.

Uwar gidan gwamnan ta kara da cewa kawo yanzu mata sama ga 422 ne suka samu lafiya daga wannan cuta ta yoyo a karkashin wannan gidauniya ta ta mai suna Maria Tambuwa Development Initiative(MTDI).

Exit mobile version