Sokoto: Tambuwal Ya Rushe Shugabannin ?ananan Hukumomi

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto, ya rushe kafatanin Shugabannin kantomomin ri?o na ?ananun hukumomi 23 dake fa?in jihar ta Sokoto.

Gwamnan ya rushe kwamitin ne ran juma’a da ta gabata jim ka?an bayan ganawar da yayi da su a gidan gwamnatin jihar ta Sokoto, a wani zaman gaggawa da ya yi da su.

Ya bayyana gamsuwarsa bisa goyon baya da kwarin gwiwa da suka ba gwamnatinsa inda ya bayyana cewa “Duk kun yi iya ?o?arin ku don tabbatar da nasarar wannan gwamnati shekaru biyu baya da kuma bayan za?e.”

“Duk kun san cewa ka’ida ta tsawon zangon mulkin ku shine wata shida, amma zuwa yanzu shekaru biyu ku kayi kan karagar mulki,’ in ji gwamnan.

“Ina sane da wasun ku za su nemi tsayawa takara. Ina yi musu fatan alheri. Ko kun dawo ko ba ku dawo ba, za mu cigaba da tuntubar juna duk sanda bu?atar hakan ta taso.”

A martanin da ya bayar tsohon shugaban ?aramar hukumar gudanarwa ta Sokoto ta Arewa, Alhaji Aminu Ibrahim, da aka fi sani da No Delay, a madadin sauran takwararorinsa, ya bayyana godiya ga gwamnan bisa dama da ya ba su na yiwa jama’ar yankunansu aiki.

“Za mu cigaba da mara maka baya saboda mun fahimci manufarka ta son cigaban al’ummar jihar nan ne.”

Related posts

Leave a Comment