Sokoto: Sarkin Musulmi Ya Nada Sabbin Hakimai

Mai alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar III, a ranar Asabar ya nada sabbin hakaimai 15 a Jihar Sokoto. Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa, NAN, ta ruwaito cewa anyi nadin ne bayan rasuwar hakiman da ke shugabancin garurruwan.

Sarkin musulmin ya taya sabbin hakiman murna kuma ya bukaci su tabbatar sun yiwa garurruwansu wakilci mai kyau a majalisar sarkin musulmin.
“Nadin da aka yi muku karin nauyi ne da kuma dama domin ku yi wa garurruwan ku hidima, saboda haka ina kira gare ku ku mayar da hankali domin tabbatar da kawo cigaban al’umma.
“Ana sa ran ku cigaba da aiki tare da mutanen ku domin tabbatar da zaman lafiya da hadin kai mai dorewa a jihar,” in ji shi.

Kazalika, Sarkin Musulmin ya yi wa sabbin hakiman addu’a sannan ya yi wa kasa addu’ar samun zaman lafiya da cigaba.

Waɗanda aka nada a matsayin hakiman sun hada da hakimin Kware, Muhammad Dan’iya, mahaifin mataimakin gwamnan jihar Sokoto da Mai shari’a Mohammed Tsamiya a matsayin hakimin Tsamiya da sauransu.

A wani labari na daban a jiya Asabar 19 ga watan Satumba 2020 Majalisar Mai Alfarma Sarkin Musulmi ta bayyana a matsayin ɗaya ga watan ga Safar na shekarar 1441 bayan hijira.

Labarai Makamanta