Sokoto: Malamin Da Ya Yi Fatawar A Kashe Matar Tinubu Ya Nemi Afuwa

IMG 20240228 WA0024(1)

Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewa wani mutumi da ya nemi a kashe matar Shugaban kasa, Remi Tinubu, saboda addininta ya janye kalamansa sannan ya nemi afuwa.

Malam Sanusi Abubakar ya ce ya yi furucin ne a lokacin yakin neman zaben shugaban kasa na 2023, domin nemawa jam’iyyarsa goyon baya kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito.

Malam Abubakar, wanda ke zaune a jihar Sokoto, ya janye kalaman nasa ne bayan ya tuntubi kungiyar kare hakkin musulmi (MURIC).

Shugaban kungiyar reshen jihar Kano, Hassan Indabawa ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa. Mun nesanta kanmu daga kalamansa, MURIC Ya ce hedkwatar MURIC ta yi Allah wadai sannan ta nesanta kanta da kalaman mutumin a ranar Juma’ar da ya yi maganar.

Indabawa ya ce: “Da yake martani ga sanarwar da MURIC ta saki a ranar Juma’a, 23 ga watan Fabrairun 2024, wani mutum mai suna Sanusi Abubakar ya tuntunbi MURIC,. “Yana mai janye duk wasu kalamansa na rashin tunani, tsokana, ganganci da ya yi na kira da a kashe Sanata Remi Tinubu, uwargidan shugaban kasa.”

Abubakar ya yarda a wasikar ban hakurinsa cewa furucinsa ba ya bisa tsarin koyarwar addinin Musulunci.
A halin da ake ciki, Indabawa ya ce kungiyar MURIC ta yi kira da a samar da ka’idojin wa’azin addini don magance kalaman kiyayya da wasu malamai ke yi.

Labarai Makamanta

Leave a Reply