Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewa Majalisar dokokin jahar a zamanta na ranar Talata ta amince da gyaran dokar Majalisar Sarkin Musulmi wadda zata rage ikon Sarkin Musulmi wurin nadawa ko cire Hakimmai, Uwayen Ƙasa da sauransu.
Majalisar ta kuma amince da gyaran dokar ƙananan hukumomi wadda zata baiwa zababbun Shuwagabanni ƙananan hukumomi da Kamsiloli damar shekaru 3 saman mulki amadadin shekaru 2.
Batun kudirin rage ƙarfin ikon Sarkin Musulmin wani al’amari ne da ya dauki hankalin jama’ar Najeriya, inda wasu malaman addini ke ganin taɓa alfarmar Sarkin Musulmin tamkar taba alfarmar addinin Musulunci ne.