Sokoto: Kusoshin PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC

Rahotannin daga jihar Sokoto na bayyana cewar Jam’iyyar APC reshen jihar tace ta sake karɓan sabon rukunin masu sauya sheka daga jam’iyyar PDP gabanin babban zaɓen 2023 da ke tafe.

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da Bashar Abubakar, kakakin Sanata Aliyu Wamakko, ya raba wa manema labarai ranar Talata a birnin Sakkwato.

A cewar Abubakar, masu sauya sheƙar sun fito ne daga ƙaramar hukumar Sabon Birni, kuma cikinsu har da Sakataren jam’iyyar PDP na shiyya, Alhaji Musa da wasu shugabanni a matakin gunduma.

“Tururuwar mutanen da ake samu suna sauya sheka (zuwa APC) wata babbar alama ce da ke nuna jam’iyya mai mulkin jihar ta zama tarihi.” Ya ƙara da jaddada kudirin jam’iyyar APC na samar da walwala da jawo kowa a jiki tare da yin aiki da gudummuwar kowane mamba domin cika muradan al’ummar Sokoto.

Masu sauya shekar sun bayyana cewa sun zaɓi rungumar APC ne domin su ba da tasu gudummuwar wajen fafutukar samun nasara a zaɓen 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply