Babbar kotu a jihar Sokoto ta dakatar da gwamnan jihar, Ahmed Aliyu daga tube rawanin biyu cikin hakimai 15 da gwamnatinsa ta tsige.
Hakiman Tambuwal da Kebbe, Alhaji Buhari Tambual da Alhaji Abubakar Kassim, wadanda ke cikin hakiman da gwamnatin jihar ta tube ne suka shigar da karar.
Gwamnatin ta dauki mataki a kan su ne bisa zargin hannu a matsalar tsaro da kuma kin yin biyayya.
Alkalin kotun, mai shari’a Kabiru Ibrahim Ahmed ya bai wa gwamnan da alkalin alkalan jihar da fadar sarkin musulmi da su soke tubewar har zuwa lokacin da za a yanke hukunci kan karar da hakiman suka shigar gabansa ta hannun lauyansu Farfesa Ibrahim Abdullahi mai mukamin SAN.
Mai shari’a Ahmed ya umarci wadanda ake kara da wakilansu da su tsaya kan matsayin da ake game da batun tsige hakiman a jihar Sokoto musamman hakiman Kebbe da Tambuwal har sai lokacin da aka kammala sauraron karar da suka shigar gaban kotu.
Tuni dai korar hakimai 15 da kudirin da ke neman yin garambawul ga dokar kananan hukumomi a Sokoto suka janyo cece-kuce a fadin Najeriya inda mataimakin shugaban kasa, Kassim Shetiima ya nemi gwamnatin jihar ta mutunta kujerar sarkin musulmi.