Sokoto: Bafarawa Da Wamakko Sun Yi Sulhu

Tun bayan kammala zaben 2007 ne alaka ta yi zafi tsakanin tsohon gwamnonin jihar Sokoto Alhaji Attahiru Tsalhatu Bafarawa da Dr Aliyu Magatakarda Wamkko har kawo yanzu, lamarin da ya kai har kowa ba ya kaunar ya ji labarin wani, kuma wannan bakar kiyayya da ke tsakaninsu ya sa ba su taba zama jam’iyya daya ba, yau idan Bafarawa yana PDP shi kuma Wamakko yana APC, idan Bafarawa yana APC shi kuma Wamakko yana PDP, haka su ke wannan adawar siyasa.

Ko a baya bayan nan ma a zaben 2019 alaka tsakanin Bafarawa da Wamakko ta kara zafi domin har sai da ta kai ga yin amfani da kafofin watsa labarai suna soke-soken junan su ta hanyar kiran junansu da wasu bakaken kalmomi, wanda hakan ya sa kiyayya da gaba a tsakanin magoya bayansu a jihar Sokoto su ma ta yi zafi.

To sai dai ranar Larabar da ta gabata (5/8/2020) ta zo wa magoyansu da mamaki, a wajen ta’aziyyar wani bawan Allah Alhaji Abbas Babi, inda aka hadu tsakanin Bafarawa da Wamakko, aka gaisa sannan kuma aka yi dariya da fara’a ga juna. Magoya bayansu dake wajen suka kama ihu da shewa da tsalle, domin ba su taba tunanin zuwan irin wannan rana ba.

Don haka kalubalen ku masu kiyayya da ‘yan uwansu akan ra’ayin siyasa, ku sani cewa su wadannan ‘yan siyasa da kuke kiyayya da ‘yan uwanku akan su kansu hade yake, dubaru ne kawai suke muku irin na ‘yan siyasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply