Ranar 29 ga watan Oktobar ta shekarar 2006 ta kasance ranar da al’ummar musulmi musamman na jahar Sokoto ba za su taba mantawa da ita ba.
Domin a wannan rana ce jirgin sama na Aviation Development Company (ADC) mai lamba 5-BEF ya yi mummunan hadari a “Tungar Magaji” jim kadan bayan da ya taso daga Abuja zuwa Sokoto dauke da muhimman mutane ‘yan asalin jahar Sokoto su 98 daga filin jirgin sama na Dr Nmandi Azikiwe dake Abuja zuwa filin jirgin sama na Sultan Abubabar dake Sokoto.
A wannan hadarin jirgin sama, al’ummar jihar Sokoto sun tafka babbban rashi domin sun rasa muhimman mutane kamar haka;
Sarkin Musulmi Muhammad Maccido Abubakar 111 MFR.
Dr Sanusi Usman Junaidu, Kwamishinan ilimi.
Sanata Badamasi Muhammadu Maccido, Sanatan Sokoto Ta Tsakiya.
Garba Muhammad Mataimakin Gwamna Bafarawa.
Alhaji Abdulrahman Shehu Shagari.
Alhaji Sule Yari Gandi, Sanatan Sokoto Ta Kudu.
Alhaji Umaru Babuga, Ciroman Dange, da sauran muhimman mutane.
Kuma insha Allahu a ranar Lahadi mai zuwa za a yi bikin tunawa da su domin yi musu addu’ar samun rahama.
Ubangiji Allah ya jikansu da rahama.