Sokoto: An Ɗaura Auren Ɗan Aliero Da ‘Yar Yarima

An ɗaura aure tsakanin ƴaƴan Sanatoci guda biyu kuma tsofaffin gwamnonin Jihohin Kebbi da Zamfara, Injiniya Sulaiman Adamu dan gidan Sanata Adamu Aliero da amaryarsa Dr. Fatima Ahmed Sani yar gidan Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura.

An daura auren a kan sadaki 100,000 a gidan yayan Yarima kuma sarkin Bakura, Alhaji Bello Ahmed Sani, a Mabera, Sokoto.

Shugaban Majalisar Mattawa, Dr. Ahmad Lawan da shugaban masu rinjaye, Abdullahi Yahayya da wasu Sanatoci hudu sun ziyarci Sokoto don halartar bikin.

Shugaban majalisar dattawan ne ya yi wa amarya Walicci, yayin da gwamnan Zamfara, Alhaji Bello Matawalle, ya yi wallicin Ango.

Daga cikin manyan mutanen da suka halarci wannan aure akwai: Sanata Aliyu Magatakarda Wammako, Sanata Bala ibn Na’allah, Sanata Ibrahim Gobir da Sanata Danbaba Dambuwa.

Ɗaurin auren ya kuma samu halartar ministan harkokin ‘yan sanda, Alhaji Muhammadu Maigari Dingyadi, da ministan Shari’a Abubakar Malami, SAN, da ‘yan majalisu da dama na jihohin Sokoto, Kebbi da Zamfara.

Wakilin Najeriya a Tanzania, Amb. Sahabi Isa Gada, tsohon ministan sufuri, Alhaji Yusuf Suleiman, da kuma dan takarar gwamna a jam’iyyar APC Alhaji A. A. Gumbi duk sun halarci taron.

Gwamnonin Sokoto, Kebbi, Zamfara da Yobe, Alhaji Aminu Waziri Tambuwal, Sanata Abubakar Atiku, Alhaji Bello Matawalle da Alhaji Mai-Mala Buni duk sun samu halartar daurin auren.

Anyi addu’o’in samun zaman lafiya ga auren da kuma kasa baki daya wanda Sheikh Bashir Gidan Kanawa ya jagoranta.

Labarai Makamanta

Leave a Reply