Sokoto: Ɗan Majalisa Ya Harbe Ɗan Fashi

Ɗan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Gwadabawa da Illela a majalisar wakilai, Abdullahi Salame ya bindige wani dan fashi har lahira, yayin da ya rauna ta abokansa a lokacin da suka je gidan shi da ke unguwar Bado a Sokoto da karfe ukun dare don yi masa fashi.

Dan majalisar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a sokoto tare da sa hotunan yadda lamarin ya kasance a shafinsa na sada zumunta.

Cikin abubuwan da ya nunawa duniya a shafin sa na sada zumunta sun hada da hula,(face cap) da wuka da gora.

Hon Abdullahi Salame dan jam’iyyar APC ne kuma shine shugaban yaki da talauci na majalisar wakilan najeriya. Ya kuma taba rike kakakin majalisar jihar sokoto daga shekarar 2007 zuwa 2011

Kakakin rundunar yan sanda reshen jihar sokoto, Muhammad Sadiq ya tabbatar da aukuwar lamarin inda ya bayyana cewar sunyi iya bakin kokarin su lokacin da suka samu labarin aukuwar lamarin, kuma zasu gudanar da cikakken bincike

Labarai Makamanta

Leave a Reply