Sokoto: ?anin Sarkin Musulmi Kwamishinan Cikin Gida Ya Rasu

Kwamishinan Ma’aikatar Lamurran Cikin Gida na Jihar Sakkwato, Hon. Abdulkadir Jeli Abubakar III ya kwanta dama bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III na daga cikin muhimman mutanen da suka halarci sallar jana’izar marigayin a daren jiya a Fadar Sarkin Musulmi.

Jeli wanda kane ne ga Mai Alfarma Sarkin Musulmi, ya rasu yana da shekaru 64 a yammacin jiya. Kafin zamansa Kwamishinan Ma’aikatar Lamurran Cikin Gida ya kasance Kwamishinan Yada Labarai.

Marigayin ya rasu ne watanni bakwai bayan da Kwamishinan Tambuwal na Ma’aikatar Filaye da Gidaje, Hon. Sirajo Gatawa ya karbi kiran mahalaccinsa.

Marigayin Kwamishinan wanda ke da sarautar Dikkon Sakkwato ya rasu ya bar matan aure biyu, ‘ya’ya da jikoki. Jama’a da dama sun bayyana shi a matsayin dattijo mai kyawawan halaye wanda ke da mutunci, son jama’a da mutunta su.

Related posts

Leave a Comment