Shugaban hukumar zaɓe Farfesa Mahmud Yakubu ya ce INEC za ta bi duk wani umarnin kotu game da sokewa ko yi wa jam’iyyun siyasa rajista a ƙasar.
Farfesa Yakubu ya bayyana hakan ne a yau Asabar yayin wani taron ƙara wa juna sani da ke gudana yanzu haka a Abuja game da babban zaɓen ƙasar da ke tafe a 2023.
Tun a watan Fabarairu na 2020 ne INEC ta soke jam’iyyun siyasa 74 a Najeriya, abin da ya hana su shiga duk wani zaɓe da za a gudanar a ƙasar.
Da aka tambaye shi game da dalilin da ya sa INEC ta soke rajistar jam’iyyar Youth Party (YP) duk da umarnin kotu, shugaban hukumar ya ce har yanzu batun yana kotu.