Labarin dake shigo mana daga Jihar Kaduna na bayyana cewar Dakarun sojojin Najeriya sun bindige wasu yan bindiga a hanyar Kaduna zuwa Zaria a karamar hukumar Igabi, ta Jihar Kaduna.
Mista Samuel Aruwan, kwamishinan a ma’aikatar tsaro da harkokin cikin gida na Jihar Kaduna, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa a ranar Laraba da ya fitar kuma aka rarrabawa manema labarai a Jihar.
“Da shigarsu wurin, sojojin suka fara yi wa yan bindigan ruwan harsashi yayin da yan bindigan suka yi kokarin mayar da martani. An kashe biyu daga cikin bata garin.” Gwamnatin Kaduna ta jinjina wa dakarun sojoji bisa kwazonsu.
Aruwan ya ce gwamnatin jihar Kaduna ta yi farin cikin samun labarin ta kuma jinjinawa sojojin saboda amsa kirar cikin gaggawa. Ya ce gwamnatin tana mika godiyarta ga dakarun sojojin da sauran jami’an tsaro yayin da ta ke karfafa musu gwiwa su cigaba da kokarin kawar da bata garin.
Aruwan ya yi kira ga al’umma su sanar da hukuma idan sun ga wani da raunin bindiga yana neman magani Ya ce tunda mafi yawancin yan bindigan sun tsere da raunin bindiga, gwamnatin na kira ga mutane su kai rahoton duk wani wanda ba a yarda da shi ba da ke neman likita.