Kotun sauraron kararrakin zabe da ke zaman ta a babban birnin tarayya Abuja, ta soke zaben gwamnan jihar Bayelsa da Gwamna Duoye Diri da mataimakinsa, Lawrence Ewhrudjakpo suka yi nasara a zaben jihar da akayi a watan nuwanban shekarara data gabata.
Alkalai uku na kotun wadandaa suka samu shugabancin Mai shari’a Ibrahim Sirajo a ranar Litinin sun sanar da wannan hukuncin bayan jam’iyyar ANDP ta kalubalanci rashin saka ta a jerin jam’iyyu a zaben da aka yi a ranar 16 ga watan Nuwamban 2019.
Gwamnan yana da damar kalubalantar wannan hukunci a kotun daukaka kara duk da Alkalan sun bayar da umarnin sake wani zaben cikin kwanaki 90,