Siyasa: El Rufa’i Ya Fallasa Asirin Peter Obi


A ranar Litinin ne gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya bayyana yadda tsohon gwamnan jihar Anambra kuma dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour, Peter Obi, ya umarci jami’an tsaro na SSS, da su kulle shi a otel na tsawon awanni 48 a jihar.

Mista El-Rufai ya ce lamarin ya faru ne a shekarar 2013 lokacin da ya je jihar a matsayin jami’in sanya ido na jam’iyyar APC, domin shaida zaben maimai na gwamnan jihar Anambra.

El Rufa’i ya bayyana hakan ne a lokacin da yake jawabi ga kwamitin hadin gwiwa na yankin Kaduna ranar Litinin tare da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu.

Ko da ya ke El-Rufai ya ce yana da dukkanin jami’an tsaro a hannunsa a matsayinsa na gwamnan jihar Kaduna a yanzu domin ya rama zaluncin da aka yi masa, amma ba zai rama mugunta da mugunta ba.

“A shekarar 2013 na je jihar Anambra a matsayin jami’in jam’iyyar APC domin shaida zaben fidda gwani na gwamna. Bakonku, Peter Obi, shine gwamna a Lokacin. Ya sa a ka tsare ni na tsawon awanni 48 a dakin otal di na.

“Yanzu ni ne gwamnan jihar Kaduna. Kuma yana zuwa Kaduna, ban da ’yan sanda da SSS, ina da shiyya-shiyya guda daya na rundunar sojojin Nijeriya a nan idan ina bukatar kamawa da tsare kowa. Amma mu ’yan Arewa ne, muna da wayewa, ba ma yin haka.”

Labarai Makamanta

Leave a Reply