Siyasa Ce Ta Sa Ganduje Ya Rufe Masallaci Na – Abdul-Jabbar Kabara

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya yi magana a kan dalilin da yake ganin shine ya sa gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shi daga yin wa’azi.

A tattaunawarsa da jaridar Daily Trust bayan Gwamna Abdullahi Ganduje ya dauki wannan matakin a kansa, Sheikh Kabara ya yi zargin cewa matakin na da nasaba da siyasa ba wai lamarin addini ba.

Malamin ya ce gwamnan ya bi ta kansa ne saboda ya yi adawa da shi a lokacin zaben gwamna na 2019 a jihar.
“Dalilan a bayyane suke. Mutumin da ya dauki hukuncin (Ganduje) ya fadi lokuta da dama cewa baya yafiya. “Na yi yaki da shi a lokacin zaben karshe da aka yi kuma ya yi alkawarin ramawa.

Illa kawai ya dauki matakin da bai dace ba a lokacin da bai dace ba. Don haka wannan haramcin siyasa ce karara, bai da wani alaka da addini.”

Da yake kira ga mabiyansa kan su shirya kuri’unsu don zabe na gaba, Kabara ya ce ainahin makiyansa sune sauran malamai, ba wai gwamnati ba inda ya kara da cewa kawai dai a yanzu jihar na aiki ne a madadinsu.

Sheikh Kabara ya kara da cewar rufe masallacinsa da hana shi yin wa’azi da gwamnatin jihar ta yi “zalunci ne”, kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito.

Malamin ya ce gwamnatin da kanta, ta bakin kwamishinan ilimi na jihar, ta tabbatar da cewa abinda ake yi masa zalunci ne amma ta dakatar da shi ba tare da bashi damar ya kare kansa ba.

Abdul-jabbar ya yi wannan jawabin ne biyo bayan rufe masallacinsa da makarantarsa da gwamnatin Kano ta yi a ranar Laraba gami da hana saka karuntunsa a gidajen rediyo da kafafen sada zumunta na jihar, bisa ga zargin sa?a ka’idar karantarwa.

Related posts

Leave a Comment