Majalisar zartarwan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ekiti ta dakatar da gwamnan jihar Ekiti, Kayode Fayemi.
Rikicin cikin gidan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Ekiti ta dau sabon salo ranar Juma’a.
A cewar jam’iyyar, an dakatad da gwamnan ne sakamakon irin yankar bayan da ya ke yiwa jam’iyyar musamman rawan da ya taka a zaben gwamnan jihar Edo da aka kammala, ChannelsTV ta samu labari.
A cikin jerin tuhume-tuhumen da suka yiwa Fayemi, mambobin majalisar zartarwa ya taimakawa gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, na People’s Democratic Party(PDP) wajen kayar da Fasto Ize-Iyamu na jam’iyyar APC.
Hakazalika, mambobin majalisar sun sanyawa shugaban jam’iyyar, Paul Omotosho, takunkumi saboda dakatad da su da yayi.Wadanda suka rattafa hannu kan takardan sune: Sanata Tony Adeniyi, Sanata Babafemi Ojudu, Sanata Dayo Adeyeye, tsohon dan majalisa, Bimbo Daramola, Robinson Ajibiye, Oyetunji Ojo, Adewale Omirin da Femi Adeleye.
Wannan dakatarwan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan dakatad da hadimin Buhari, Sanata Babafemi Ojudu, da wasu mutane 10.