Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya dora laifin halin da kasar ke ciki a kan shugabannin Najeriya da suka gabata, ya ce sun “kusa rusa kasar.”
Koda dai Shugaban kasar bai ambaci sunan shugabannin ba, ya yi hannunka mai sanda ga wadanda suka mulki Najeriya a tsakanin 1999 da 2015, inda ya dasa ayar tambaya kan yadda aka yi har shugabannin suke da bakin sukar gwamnatinsa.
“Wadanda suka yi mulki daga 1999-2015, wadanda suka kusa durkusar da kasar a yanzu sune suke yunkurin sukar kokarinmu.”Shugabannin Najeriya tun daga 1999 sune Olusegun Obasanjo (1999 zuwz 2007), Marigayi Umaru Yar’Adua (2007 zuwa 2010), Goodluck Jonathan (2010 zuwa 2015).
Jawabin na ranar Alhamis ya kasance karo na farko da shugaba Buhari ke martani da kansa tun bayan sukar gwamnatinsa da Obasanjo yayi a baya-bayan nan.
Ko a makon da ya gabata mun kawo maku ruhoto kan yadda tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi korafi a kan tabarbarewar tsaro da kuma halin da tattalin arzikin kasar ke ciki, inda ya daura laifin a kan gwamnatin Buhari.