Shugabancin Tinubu Rahama Ne Ga ‘Yan Najeriya – Shettima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bayyana cewa samuwar Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya, ba sa’a ko gam-da-katar ba ne, wata mu’ujiza ce daga Allah maɗaukakin Sarki.

Kashim ya ce Allah ya bai wa Najeriya shugaba mai tsarkakkar zuciya, shi ya sa ya zama shugaban ƙasa.

Shettima ya bayyana haka ranar Juma’a, lokacin da ya karɓi baƙuncin tawagar shugabannin Hukumar Aikin Alhazai ta Kiristoci, wato NCPC, waɗanda suka kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa, a Abuja.

“Dajin da muka keto har Shugaba Bola Tinubu ya samu nasara ba sa’a ba ce kaɗai ko wani gam-da-katar.

“Tinubu mutum ne da ya daɗe ya na taka rawar ganin ciyar da ƙasar nan gaba.

“Nasarar lashe zaɓen da Shugaba Tinubu ya samu, wata mu’ujiza ce daga Allah. Kuma sakayya ce Allah ya yi masa, saboda zuciyar sa tsarkaka ce,” inji Kashim Shettima.

Mataimakin Shugaban Ƙasa ya jaddada muhimmancin shugabanni wajen ɗinke ɓaraka da gina gadar haɗe mabambanta wuri ɗaya, domin hakan zai kawo zaman lafiya da ci gaban al’umma.

“To shi kuwa Shugaba Tinubu ya sadaukar da kan sa, kuma ya ɗinke ɓaraka. Kuma ya kasance mutumin da aka riƙa yi wa bi-ta-ƙullin siyasa, har Allah ya Allah ya sa ya zama Shugaban Ƙasa.

“Ko lokacin da sauran gwamnoni suka riƙa kai gwauro su na kai mari wajen tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo, shi kuwa Tinubu sai ya kafa jam’iyyar siyasa mai hangen nesa da tsinkaye,” inji Shettima.

Daga nan ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su ci gaba da juriya da kuma bai wa Shugaba Tinubu uziri da lokaci, yayin da ya ke ƙoƙarin tattabar da samun nasarar fatattakar ƙalubalen da ke addabar ƙasar nan baki ɗaya.

“Saboda shi dai Shugaba Tinubu ba wai tsautsayi ne ya kai shi mulkin ƙasar nan, ko sa’a ko gam-da-katar ba. Shi mu’ujiza ce daga Allah.”

Daga nan ya yi kira ga sabbin shugabannin hukumar Alhazan Kiristoci ta Najeriya su ci gaba da jajircewar wajen yin aiki tuƙuru.

Ya tunatar da shugabannin hukumar muhimmancin addini wajen shawo kan ƙalubalen da ƙasa ke fuskanta.

Tun da farko, Babban Sakataren NCPC, Stephen Adegbite, wanda babban limamin Majami’a ne, ya fara da godiya ga Shugaba Tinubu, saboda damar da ya ba su, domin yin aiki a hukumar.

Haka kuma ya yabi Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, bisa shugabanci nagari da ya yi a lokacin da ya na gwamnan Jihar Barno.

“Lokacin da muka je Maiduguri, ni ne Daraktan Al’amurran Ƙasa na Ƙungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN).

“Shugaban CAN na Jihar Barno a lokacin, ya shaida mana irin irin ayyukan alherin da ka yi wajen goyon bayan Kiristocin Jihar Barno.

“Ka gina masu coci-cocin da Boko Haram suka rushe masu,” inji shi.

Ya ce Mataimakin Shugaban Ƙasa, Shettima, ya kasance ya na bai wa coci-coci goyon baya, kuma ya na tabbatar da an samu zaman lafiya da fahimtar juna a coci-cocin Najeriya da sauran mabiya wasu addinan a Najeriya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply