Shugabancin Najeriya: Kuskure Ne Zaɓar Wanda Ya Haura 50 – Shugaban Matasa

An bayyana cewar yanayi ya sauya matuƙa wanda muddin ana bukatar abubuwa su sauya a ƙasar nan to ya zama wajibi a yi la’akari da shekaru a wajen zaɓen Shugabannin musamman Kujerar shugaban ƙasa, matukar Mutum ya zarce shekaru 50 to a cire shi cikin lissafi.

Shugaban gamayyar Kungiyoyin matasan Arewacin Najeriya Alhaji Nastura Ashir Sherif ne ya bayyana hakan, a yayin wata tattaunawa da ya yi da wakilinmu ta wayar tarho a garin Kaduna.

Shugaban Matasan ya ƙara da cewar Shekaru wasu abubuwa masu muhimmanci a shugabanci wadanda ya dace ayi la’akari da su, idan ya zamana an zaɓi Shugaban ƙasa wanda bai haura 50 ba, shi kuma ya naɗa Shugaban ma’aikatan shi mai shekaru 60-65, babu shakka za’a samu natija mai kyau, inda zai zamana duk lokacin da shugaban ya karkace shi to shi Shugaban ma’aikata kasancewar ya fishi gogewa da kwarewa akan harkar rayuwa zai dawo da shi bisa turba.

Dangane da bikin tunawa da ‘yan Mazan jiya da aka saba gudanarwa a kowace shekara 15 ga watan Janairu kuwa, Ashir Sherif ya ce yin hakan abu ne da ya dace a rinƙa gudanar da taro domin tuna kokari da bajimtar da magabata suka yi, kuma tabbas wadannan magabata misali Firimiyan Arewa na farko kuma na ƙarshe Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto da Abubakar Tafawa Balewa sun yi wa kasar nan da yankin Arewa hidima wadda har abada ba za’a manta da ita ba.

“Ina tabbatar maka ba domin wadannan shugabanni ba to da a yanzu ɗan Arewa na matsayin Bawa a Najeriya wanda sai dai ya yi aikin karfi wajen kula da kanshi amma ba ma’aikaci a ma’aikatun gwamnati ba musanman na gwamnatin tarayya.

Labarai Makamanta