Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David, ya zargi dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Bola Ahmed Tinubu, da kokarin raba kawunan Kiristoci da mabiya coci.
Babachir ya bayyana cewa a kokarinsa na ganin ya shawo kan masu zabe sun yarda da tikitin addini guda, Tinubu ya tanadi kungiyoyin kirista na bogi don raba kan coci, da shiga abin da ya kira Hauma-Hauma.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayyan ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa dauke da sa hannunsa wanda aka gabatarwa da manema labarai ta hannun tawagar yada muradunsa, a birnin tarayya Abuja.
“Zuwa yanzu dai bamu dauki hanyar sulhu ba saboda a matakin farko, daga APC a matsayinta na jam’iyya har dan takararta da shugaban kasa basu damu da neman yin sulhu da mu ba duk da cewar mun bayar da kafar yin haka.
“Kawai dai mun ji ra’ayoyinsu ne ta farfaganda da ake yadawa a kafofin watsa labarai bisa la’akari da yawan sukar da suke sha. “Shakka babu akwa wasu kiristoci wadanda saboda dakushewar dabi’a, talauci ko hadama suka bayar da hayar kansu a matsayin wakilai da masu bata addinin kiristanci.”