Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya ce kada yan Najeriya su kuskura su zabi mutumin da bai da lafiya a matsayin shugaban kasa a babban zabe mai zuwa.
Obi ya bayyana hakan ne a jami’ar Najeriya da ke Nsukka, jihar Enugu a ranar Alhamis, 12 ga watan Janairu.
Dan takrar na LP ya bayyana Najeriya a matsayin kasa mara lafiya, cewa bai kamata a zabi mutumin da bai da lafiya a matsayin shugaban kasar ta ba a zaben shugaban kasa mai zuwa.
Ya kuma ce bai kamata yan Najeriya su zabi kowane dan takarar shugaban kasa da ba zai iya tsayawa na tsawon mintina 30 ba.
Har wayau, Obi ya bukaci yan Najeriya da su duba halayya da aminci a babban zaben 2023 don gudun jefa kasar cikin karin matsala. “Kasar nan bata da lafiya kuma bai kamata a mikata a hannun mara lafiya ba. “Ba wai ina cewa wani bai da lafiya bane. Muna nan fiye da awa biyu, ba ma son mutane da ba za su iya tsayawa na mintuna 30 ba.