Shugabancin Kasa: Duk Wanda Ya Haura 70 Ya Ja Da Baya – Matasan Arewa

Kungiyar cigaban Matasan Arewacin Najeriya jihohi 19 har da Abuja, ta yi tsokaci dangane da halin da siyasar kasar nan ke fuskanta inda ya zamana tsofaffi ne ke ta karba-karba a tsakaninsu tare da yin watsi da matasa, bisa ga haka kungiyar ta ja layi ta bayyana ba zata lamunci haka ba, lallai duk tsohon da ya haura 70 ya koma gefe kawai.

Kungiyar ta bayyana hakan ne a cikin wata takardar sanarwa wadda ta samu sanya hannun Shugaban ?ungiyar na kasa Alhaji Imrana Nas kuma aka rarrabata ga manema labarai a birnin tarayya Abuja.

Matasan na Arewa sun cigaba da cewar abin damuwa ne da takaici yadda Najeriya take tsaye wuri guda ba ta gaba ba ta baya dalilin shugabancin tsofaffi, hakan ya sanya a kowace rana abubuwa ?ara dagulewa suke yi a ?asar, tabbas lokaci ya yi da wadannan dattawa za su kauce su ba Matasa dama su gwada tasu bajintar.

Sun bada misali da halin da Najeriya ke ciki yanzu ?arkashin jagorancin shugaban ?asa Buhari, sakamakon tsufa ya zamana bai san abubuwan da ke tafiya a kasar ba, sai abin da aka gaya mishi kawai shi ya sanya kullum abubuwa ke ?ara ta?ar?arewa a ?asar.

Matasan wa?anda suka koka akan abin da suka kira zalunci da son Zuciyar shugabanni musanman a yankin Arewa, sun bada misali da irin dattaku da Shugaban Arewa na farko Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ya yi, ta hanyar gina ‘yan Arewa ba tare da la’akari da asalin mutum ba, yawa yawan wadannan ‘yan Arewa da Sardauna ya gina sune suka zama jagorori a ?asar, amma abin takaici su sai suka yi wa ‘yan baya bu?ulu da butulci, suka mayar da hankali akan ‘ya’yan su da dangin matansu kawai.

Matasan na Arewa sun ?ar?are da cewar matakin da suka ?auka ya shafi dukkanin kasar ne, lallai duk wani mai jini a jika da ya cancanta ya zama shugaba daga ko ina ya fito a ?asar zasu mara mishi baya domin kai wa ga nasara.

A halin da ake ciki dai yanzu wa?anda suka fara nuna aniyar tsayawa takarar sun ha?a da tsohon mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Legas Bola Tinubu da mataimakin Shugaban kasa Osinbajo, wanda dukkanin su ake kallon shekaru sun yi musu yawa.

Related posts

Leave a Comment