Shugabancin Kasa: Babangida Na Goyon Bayan Atiku – Dino Melaye

Labarin dake shigo mana daga jihar Delta na bayyana cewar Tsohon Sanata daga Jihar Kogi kuma jigo a Jam’iyyar PDP Dino Melaye, ya bayyana cewar tsohon Shugaban ƙasa Ibrahim Badamasi Babangida na goyon bayan takarar shugaban kasa na Atiku Abubakar a zaben da ke tafe.

Ta shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 27 ga watan Janairu, Melaye, mai magana da yawun kwamitin kamfen din shugaban kasa na jam’iyyar PDP, ya ce an tabbatar da hakan a Jihar Delta ranar Laraba, 25 ga watan Janairu, yayin kaddamar da wani aiki da Atiku ya yi.

Melaye ya yi ikirarin cewa Babangida ya sanar da matsayinsa ta bakin dansa ne, Mohammed. “Muna son mu gode wa iyalan tsohon shugaban kasa na mulkin soja Ibrahim Badamasi Babangida saboda goyon bayan Atiku a matsayin shugaban kasar Najeriya.

“Mohammed Babangida ne ya bayyana hakan a Jihar Delta a ranar Laraba yayin kaddamar da filin fina-finai da shakatawa na Maryam Babangida, Inji Dino Melaye.

Labarai Makamanta

Leave a Reply