Shugabancin INEC: Majalisa Ta Tabbatar Da Tazarcen Yakubu

Majalisar dattawa ta tabbatar da sake nada Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin Shugaban hukumar zabe ta Nijeriya INEC a karo na biyu.

A ranar Litinin 9 ga Nuwamban nan ne Farfesa Mahmud Yakubu, ya mika ragamar shugabancin hukumar ga Air Vice Marshal Ahmed Mu’azu mai ritaya a matsayin shugaban riko kafin majalisar ta sake amincewa da nadinsa.

A watan Oktoban shekarar 2015 ne dai Shugaban kasa Buhari ya na?a Farfesa Yakubu a matsayin shugaban hukumar ta INEC, kuma shi ne ya jagoranci babban zaben kasar na shekarar 2019.

Wani shawara zaku ba shugaban hukumar zabe musamman akan yadda yake gudanar da zabuka a fadin kasar nan?

Related posts

Leave a Comment