Jam iyyar PDP tace ta gano abun da yasa shugaban kasa Muhammad Buhari ya kara nada Prof. Mahmood Yakubu a matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa.
Jam iyyar tace wannan sake nadin da aka wa Prof. Yakubu zai shafi , rayuwar mutanan Najeriya sama da mutane miliyan 200 kai harma da wanda suke ciki basuzo duniya bama.
A wanan shekaru biyar din da zaiyi gaba, jamiyyarmu tana fatan zai gyara kurakuransa, magudi da rashin gaskiyar da aka tafka a baya.
Ya kamata ya sani wannan damar da aka sake basa, ya kamata Prof. Yakubu ya wanke kansa , ta hanyar gudanar da zabuka masu nagarta , sashihai a kasar nan.
Yanzu dai, tunda ai maidasa kan kujerarsa muna fatan zabukan gaba zasu zama nagartattu domin ya riga ya gama sanin duk yadda hukumar INEC take.
Dadin dawa, mun dauki wannan hukuncin na shugaban kasa Buhari a matsayin wani yunkuri na wanke kansa wajen ganin an gudanar da sashishin zabe kamar yadda yake fada kullum, inda yake cewa zai gudanar da sashihi kuma nagartaccen zabe a 2023 idan zai sauka.
Muna kira ga hukumar INEC da tayi amfani da guntun shekaru biyun da suke gabanta wajen yiwa hukumar gyara, kawo dabarun da zasu gyara sabgogin zaben ,da saka hannu akan sabbun dabarun zabe da majalissa wakilai ta amince dasu .
muna fatan Prof. Yakubu zai gudanar da ayyukansa fiye da tunaninmu.
Dama mafi yawancin yan Najeriya sunyi zaton haka. Don haka sai ya dage wajen ganin ya kawo karshen magudi, rigimgimu,da kuma tsinka zabuka kamar yanda ya gudanar a zangon mulkinsa na farko.
Ya kamata Prof. Yakubu ya sani,zaman lafiyar kasarmu yana hannunsa domin sashihin zabene kawai zai tabbatar da hakan.
Muna kira ga yan majalissa , musamman sanatoci dasu tabbatar an gyara kura kuran da akayi a baya lokacin da suke kara tantance Prof. Yakubu.