A yau Litinin ne ake sa ran cewa babban Shugaban rundunar ‘yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, da dumbin wasu manyan jami’ai zasu yi ritaya daga aiki.
Shugaban ‘yan Sandan Mohammed Adamu da sauran manyan jami’an zasu yi ritaya ne saboda sun ƙarewar wa’adin lokacinsu na aiki, kamar yadda doka ta tanada.
Adamu, wanda ya shiga aikin dan sanda a ranar 1 ga watan Fabarairu na shekarar 1986, zai yi ritaya sakamakon cika shekaru 35 yana aiki.
A watan Janairu na shekarar 2019 tsohon shugaban ‘yan Sanda Ibrahim Idris ya mika ragamar tafiyar da al’amuran rundunar ‘yan sanda ga Mohammed Adamu.
Bayan shi kansa Mohammed Adamu, akwai manyan mataimakansa (DIGs) guda uku da wasu sauran mataimakansa (AIG) guda goma da zasu yi ritaya daga aiki.
Manyan mataimakan sun hada da tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Lamurde, Aminchi Baraya, da Nkpa Inakwu. Sauran mataimakan (AIGs) sun hada da; Nkereuwem Akpan, Olafimihan Adeoye, Agunbiade Labore, Undie Adie, Olugbenga Adeyanju, Asuquo Amba, Mohammed Mustapha, Jonah Jackson, Olushola Babajide, da Yunana Babas.
A ‘yan kwanakin baya bayan nan ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sanya hannu akan sabuwar dokar da zata tilasta duk wani dan sanda yin ritaya idan ya kai shekaru 60 a duniya ko kuma shekaru 35 yana aiki.
Bisa al’adar gwamnati, akan sanar da sabon Shugaban ‘yan Sanda yayin da ya rage saura kwanaki wanda yake kai ya sauka.
Sai dai, har yanzu babu wata sanarwa daga fadar shugaban kasa dangane da batun nadin sabon Shugaban duk da saura sa’o’i kaɗan na kai ya yi murabus.