Mukaddashin sufetan ‘yan sandan Najeriya, Usman Baba, ya ba da umarnin janye manyan jami’an ‘yan sanda masu mukamin Cif Sufuritandan da suke aiki tare da jami’an hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC.
A wata wasika mai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Idowu Omohunwa, wacce ya aike wa hukumar EFCC a ranar 15 ga watan Afirilu, mukaddashin sufeton ‘yan sandan ya ce ‘yan sandan su dawo bakin aiki a ranar Laraba.
Wasikar ta ci gaba da cewa ‘’Bisa umarni sufeton ‘yan sanda, ina mai farin cikin sanar da shugaban hukumar EFCC cewa maigida ya ba da umarnin janye manyan ‘yan sanda masu mukamin Cif Sufuritanda da ke aiki ?ar?ashin hukumarku.
An dauki matakin ne saboda bukatar hakan da ta taso, muna bukatar ka ba da umarnin dawo da jami’an ‘yan sandan bakin aikinsu a ranar Laraba 21 ga watan Afirilu.’’