Shugaban Rasha Ya Bada Umarnin Tsagaita Wuta A Yaki Da Ukraine

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayar da umurnin tsagaita buɗe wuta na sa’a 36 a Ukraine, farawa daga gobe Juma’a.

Umurnin tsgaita buɗe wutar da zai fara aiki daga 12 na dare agogon Moscow, na zuwa lokacin da kiristoci ‘yan darikar Orthodox a ƙasar Rasha ke bikin kirsimeti.

Putin ya bukaci Ukraine da ta yi na’am da hakan, amma Kyiv ta mayar da martani nan take na yin watsi da bukatar.

Umurnin mista Putin na zuwa ne bayan da shugaban cocin ‘yan darikar Orthodox a Rasha, Patriarch Kirill ya bukaci tsagaita buɗe wutan a safiyar yau Alhamis.

Kiristoci ‘yan darikar Orthodox a Rasha na gudanar da bikin kirsimeti ne a ranar bakwai ga watan Janairu kamar yadda yake a kalandar Julian.

Labarai Makamanta

Leave a Reply