Shugaban Kasa Zai Rusa Kamfanin NNPC

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya gabatar da kudirin sake fasalin Kamfanonin matatun mai na shekarar 2020 (PIB) a gaban ‘yan majalisar tarayya. Rahoton ya bayyana cewa wannan kudiri zai bada damar kafa sabon kamfanin man Najeriya.

A dalilin haka kuma za a yi fatali da kamfanin man NNPC. Idan wannan kudiri ya samu karbuwa kuma har ya zama doka, gwamnati za ta soke hukumar PPPRA mai alhakin tsaida farashin kayan mai a Najeriya.

Wannan kudiri ya ba Ministocin kudi da na man fetur ikon ganin yadda za ayi gwanjon dukiyoyi da duk kadarorin NNPC ga sabon kamfanin da za su gaje su.

Kamar yadda aka bayyana, sashe na 54 (1, 2 da 3) ne su ka ba Ministocin kasar wannan iko. Da zarar an gama maidawa wani kamfani duka kadarori da dukiyoyin da NNPC ya mallaka, ko kuma aka maida su ga gwamnatin, za a ruguza kamfanin man.

Sashe na 53 na wannan kudiri ya na cewa ne:

“A cikin watanni uku da kawo wannan doka, Minista zai kafa sabon kamfanin da za a kira NNPC Limited.”
“Mallakar hannun jari ne da ya ke NNPC ya na kan wuyan gwamnati a karkashin ma’aikatar kudi.”

Gwamnati za ta raba kanta daga aikin tace danyen mai. Wannan kudiri har ila yau zai bada damar kafa wata hukuma wanda za ta rika kula da kayan mai. Za a kira hukumar Nigerian Upstream Regulatory Commission.

Bayan haka, sashe na 29 na kudirin ya na so a kafa wata takwarar hukumar mai suna Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority.

Haka zalika wannan kudiri na PIB da ake jira tun 2000, zai soke ayyukan PPPRA. Wadannan sabbin hukumomi da za a kafa, za su rika kula da farashin mai.

Kwanakin baya kun ji cewa Mai girma shugaba Muhammadu Buhari ya amince da nadin wasu sababbin shugabanni na kamfanin mai na kasa watau NNPC.

Wadannan shugabannin sun hada da Mohammed Lawal, Tajudeen Umar, Adamu Mahmood Attah, Garba Shehu, Magnus Abe, Stephen Dike da Pius Akinyelure.

Labarai Makamanta