Shugaban Kasa Ya Sanya Hannu A Kasafin Kudin Shekarar 2023

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ƙasar wanda ya kai jimillar naira tiriliyan 21.83.

Shugaban ya sanya hannu kan kasafin kuɗin ne a wani ƙwarya-ƙwaryan buki da aka yi ranar Talata a fadarsa da ke Abuja.

Hakan na zuwa ne kwana shida bayan majalisar dokokin ƙasar ta amince da kasafin.

Kasafin ya ƙunshi naira tiriliyan 6.6 na biyan bashin da ake bin ƙasar, da naira tiriliyan 8.3 na ayyukan yau da kullum, sai kuma naira tirilayn 5.9 na manyan ayyuka.

Wasu ɓangarorin da suka samu kaso mafi tsoka su ne ma’aikatar tsaro wadda aka ware wa naira biliyan 285, da ma’aikatar lafiya mai naira biliyan 134.9, da ma’aikatar makamashi mai naira biliyan 195.5, sai ma’aikatar ilimi wadda ke da naira biliyan 153.7.

A lokacin sanya hannu kan kasafin kuɗin, shugaba Buhari ya ce ya lura da cewa majalisar dokoki ta sanya wasu ƙarin ayyuka a cikin kasafin, inda ya ce ya sanya hannu ne domin samun damar fara aiwatar da kasafin cikin hanzari.

Buhari ya kuma buƙaci majalisar da ta sake duba buƙatar da ya gabatar mata na amincewa da basukan da gwamnati ta karɓa daga babban bankin ƙasar (CBN).

Labarai Makamanta

Leave a Reply