Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin aiwatar da cikakken rahoton Oronsaye wanda tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kafa tun a 2011, a kokarin gwamnati na rage yawan kashe kudaden gudanarwa.
An dai kafa kwamitin ne a lokacin sake fasalin tsarin mulki da kwamitoci da hukumomin gwamnatin tarayya karkashin shugabancin tsohon shugaban ma’aikata na Najeriya, Stephen Osagiede Oronsaye.
Kwamitin ya gabatar da rahoto mai shafuka 800 a ranar 16 ga Afrilu, 2012, inda ya bankado yadda ake gudanar da gasa a tsakanin hukumomi da dama, wanda ba wai kawai ya haifar da rashin kwanciyar haknali a tsakanin hukumomin gwamnati ba, har ma ya haifar da almubazzaranci.
Rahoton ya ba da shawarar dakatar da tallafin da gwamnati ke bai wa wasu hukumomi da majalisu wajen bayar da kuɗi don gudanar da manyan ayyuka.
Rahoton na Oronsaye ya tabbatar da cewa akwai ma’aikatun gwamnatin tarayya 541 da kwamitoci da hukumomi (na doka da na shari’a), inda ya bayar da shawarar cewa a mayar da 263 daga cikin ma’aikatun zuwa 161, yayin da rahoton ya ce a soke hukumomi 38 sannan a hade guda 52.