Shugaban Kasa Ya Aza Tubalin Ginin Jami’ar Izala

Shugaba Muhammadu Buhari ya assasa tubalin ginin jami’ar musulunci ta As-Salam Global University, Hadejia jihar Jigawa mallakar kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’ah Wa’iqamatis Sunnah, JIBWIS.

Shugaban ƙasar wanda ministan sadarwa , Dakta Isa Pantami ya wakilta ya assasa tubalin ginin jami’ar a wurin taron. Buhari shine baƙo na musamman wurin taron yayin da Sarkin Musulmi, Sultan Muhammad Sa’ad Abubakar shine shugaban taron.

Kazalika, gwamnonin da suka hallarci taron sun hada da Muhammadu Badaru na jihar Jigawa da gwamnonin Sokoto, Kebbi, Katsina, Kano da tsaffin gwamnonin Zamfara.

Kazalika, ƴan majalisa, masu sarautun gargajiya, shugabannin addini, manyan ma’aikatan gwamnati da masu tallafawa al’umma sun hallarci taron.

Da ya ke jawabi wurin taron, shugaban JIBWIS na ƙasa, Sheikh Bala Lau ya sake jaddada cewa jami’ar ta al’ummar musulmi ce. Ya ce: “Hakan yasa muke gayyatar musulmi a duk inda suke su zo su taimaka da duk abinda Allah ya sawwake musu.”
“A yayin da muke fara wannan katafaren aikin, kowa ya sani cewa fatan mu shine kafa jami’ar ingantacciya da za ta amfani dukkan al’ummar musulmi. Da fatan Allah ya mana jagora.

Labarai Makamanta

Leave a Reply