Shugaban Kasa Buhari Zai Tafi Ganin Likita Birnin Landan Yau Juma’a

Rahotanni daga birnin tarayya Abuja na bayyana cewar Fadar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta ce shugaban zai tafi birnin Landan na ƙasar Birtaniya yau Juma’a don duba lafiyarsa.

Mai taimakawa shugaba Buhari kan harkokin yaɗa labarai Femi Adesina ne ya sanar da hakan cikin wata gajeruwar sanarwa da ya fitar jiya Alhamis wadda aka rarraba ta ga manema labarai a Abuja.

Sanarwar ta bayyana cewar ana sa ran shugaban zai koma gida Najeriya a mako na biyu na watan Yuli mai kamawa bayan kammala duba lafiyar tashi.

Shugaban ƙasa Buhari ya kasance yana ziyarar birnin Landan duba lafiyar shi a kowace shekara tun bayan hawa karagar Shugabancin Najeriya da ya yi a shekarar 2015.

Labarai Makamanta

Leave a Reply