Shugaban Dakarun Soji Ya Ba Sojoji Awa 48 Su Kwato Garin Marte

Babban Hafsan sojin Nijeriya Manjo-Janar Ibrahim Attahiru ya umarci rundunar sojojin ‘Operation Lafiya Dole’ da su tabbatar sun kwato garin Marte wanda ‘ya’yan kungiyar Boko Haram suka kwace a hannun sojojin a ranar Juma’a.

Manjo Attahiru ya ba rundunar sojin wa’adin awanni 44 su tabbatar sun kwato kauyen a hannun ‘yan Boko Haram.

Attahiru ya kuma umarci rundunar sojin da su tabbatar da ingantaccen tsaro a kauyukan da suka yi mahada da garin na Marte, kamar su Kirenowa, kirta, Wulgo, Chikingudo da duk suke cikin karamar hukumar Ngala a jihar Borno.

Manjo-Janar Attahiru ya bada wannan umarnin ne a lokacin da yake wa rundunar sojoji ta tara a garin Dikwa.

Related posts

Leave a Comment