Shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmi Ya Ziyarci Najeriya

Shugaban Bankin Raya Ƙasashen Musulmai IsDB, Dr Muhammad Sulaiman Al Jassar ya kai ziyara Najeriya.

Dr Jassar ya fara ziyarar aikin ta kwanaki uku ne a ranar Lahadi 23 ga watan Oktoba.

Lokacin ziyarar, shugaban bankin gana da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, zai kuma gana da Ministar Kudin da kasafi ta Najeriya Zainab Shamsuna Ahmed, domin tattauna batutuwan da suka shafi bunkasar tattalin arziki.

Al Jassar yana ziyarar ne tare da manyan abokan hulda daga ciki har da, Bankin kasa da kasa na bunkasa fannin noma a Afirka.

Sannan gwamnati za ta kaddamar da wasu wurare da aka ware domin sarrafa amfanin gona a Najeriya, kuma IsDB ta ba da tallafin dala miliyan 160.

Labarai Makamanta

Leave a Reply