Shugaba Muhammad Buhari ya amince da nadin Imaan Sulaiman-Ibrahim a matsayin sabuwar darakta janar ta hukumar hana safarar bil’adama ta kasa NAPTIP.
Mrs Imaan ‘yar asalin jihar Nasarawa, ta yi digirin farko akan nazarin halayyar bil’Adama, digiri na biyu a kan dabarun mulki.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Malam Garba Shehu, mai magana da yawun shugaban kasa, ta ce kafin nata, mai ba karamin ministan ilmi shawara ce ta musamman kan tsare-tsare da sadarwa.