A ranar Alhamis ne Shugaba ƙasa Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2021 yayin wani zama na musamman da ya hada mambobin majalisar dattijai da na wakilai wuri guda.
Shugaba Buhari ya bayyana cewa bullar annobar korona ya taba tattalin arzikin Najeriya, sannan ya kara da cewa faduwar farashin danyen mai ta hana gwamnati samun isassun kudin shiga.
Buhari ya gabatar da kasafin kudi na N13.1trn, hakan ya nuna cewa an samu karin kaso 20% a kan adadin kudin da gwamnati ta yi kasafi a baya.
A cewar Buhari, akwai gibin N4.8trn a cikin kasafin, wanda ya bayyana cewa gwamnati za ta cike gibin da rance daga ketare.
“An yi hasashen cewa kudaden da gwamnati ta ke samu a cikin gida (GDP) za su ragu a watannin karshe na wannan shekarar da mu ke ciki.
“A saboda haka, tattalin arzikinmu zai iya sake komawa cikin wata masassarar a karo na biyu cikin shekaru hudu, wanda hakan zai zo da wasu wahalhalu.
“Sai dai, duk da haka, mu na aiki tukuru domin kirkirar hanyoyin farfado da tattalin arzikinmu a cikin shekarar 2021. “Za mu mayar da hankali wajen kaddamar da shirye-shirye da za su bawa gwamnati damar tsamo ‘yan Najeriya miliyan 100 daga kangin talauci a cikin shekaru 10 ma su zuwa,” a cewar Buhari.