Shekaru Masu Albarka: Buhari Ya Cika Shekaru 80 A Duniya

Rahotannin dake shigo mana daga birnin tarayya Abuja na bayyana mana cewar a Asabar ne 17 ga watan Disamban shekara ta 2022 shugaban kasa Muhammadu Buhari ya cika shekara 80 da haihuwa.

An haifi shugaba Buhari ne a ranar 17 ga watan Disamba a garin Daura na masarautar Daura da ke Jihar Katsina.

Tuni manyan mutane Sarakuna, Malamai da ‘yan siyasa suka soma tura sakon taya murna ga shugaban kasar.

Cikin wadanda suka soma aike sakon murnarsu ga shugaban akwai dan takarar shugabanci kasa a inuwar Jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu da kuma shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila.

Shugaba Buhari ya kafa tarihi a Najeriya a matsayin shugaban ƙasa tilo da ya samu so da ƙauna daga dukkanin ‘yan Najeriya a kyautata zaton da suka yi mishi na wanda zai tsamar dasu daga halin ƙunci da suke ciki.

Buhari ya shiga Siyasar Najeriya a shekarar 2002 a ƙarƙashin Jam’iyyar APP inda ya tsaya takarar shugabancin kasar a shekarar 2003 tare da tsohon shugaban kasa Obasanjo, amma bai samu nasara ba.

Ya sake tsayawa takara a shekarar 2007 a ƙarƙashin Jam’iyyar ANPP inda suka fafata da tsohon shugaban kasa Umaru Yar’adua nan ma bai samu nasara ba. Hakazalika ya sake takara a shekarar 2011 a jam’iyyar CPC inda tsohon shugaban kasa Jonathan ya yi nasara a kanshi.

A shekarar 2015 Buhari ya sake tsayawa takara a karo na huɗu ƙarƙashin Jam’iyyar APC inda ya yi nasara akan shugaba Jonathan da ke kan kujera, bayan kammala wa’adin zango na farko shugaban ya yi tazarce a shekarar 2019 inda zangon ke zuwa karshe a shekarar baɗi ta 2023.

Labarai Makamanta

Leave a Reply