Shekaru 60: CORONA Za Ta Rage Armashin Bukukuwa – Lai Mohammed

Lai Mohammed, ministan yada labarai da al’adu, ya ce mulkin kasar nan karkashin shugaban kasa Muhammadu Buhari, na kokarin saka kasar nan a hanyar da ta dace.

A yayin jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis domin bayyana shirye-shiryen shagalin bikin cikar Najeriya shekaru 60, Mohammed ya ce tun bayan samun ‘yancin kasar, an fuskanci yakin basasa, rikicin siyasa da kuma rashin tsaro.

Ministan ya ce wannan mulkin ya zo da sabon cigaba. “Wasu za su iya fara tunanin me yasa Najeriya za ta yi wannan shagalin bikin, ganin cewa akwai manyan kalubale da kasar ke fuskanta,”
“Hakazalika, a wasu al’adu, ana kallon shekaru 60 a matsayin tushen rayuwa kuma hakan yasa ake bikinta.

Ga Najeriya, mulkin shugaba Buhari shine tushen cigaba. “Gwamnatinsa na aiki tukuru wurin tabbatar da samuwar sabuwar Najeriya, saka tushen cigaba da fasaha ta hanyar samar da kayayyakin more rayuwa da suka hada da wutar lantarki, tituna, gada da layikan dogo da sauransu.

“Mulkin na karawa da yakar rashawa, rashin tsaro da kuma fadada hanyar tabbatar da tattalin arziki ta hanyar noma da kiwo tare da hako ma’adanai da sauransu,”

Ministan ya tabbatar da cewa, shagalin cikar Najeriya shekaru 60 za a yi ba tare da gagarumin taro ba.
“Hakan yana da alaka da annobar korona da ta gallabi duniya, wacce ta sa kowacce kasa take kokarin dakile yaduwar cutar. Hakan yasa za a rasa wasu daga cikin shagulgulan murnar,” yace.

Labarai Makamanta

Leave a Reply