A rana mai makar ta yau ne Allah ya yi wa Alhaji Shehu Kangiwa tsohon gwamnan jihar Sokoto cikawa.
Alhaji Shehu Kangiwa ya rasu a ranar 17/11/1981 a filin wasan kwallon dawaki wato Murtala square dake a cikin Birnin Kaduna.
Allah Sarki idan muka yi duba da mulkin Shehu Kangiwa da kuma ayukkan da ya yi a lokacin sa lokacin da jihohin Kebbi, Sokoto da kuma Zamfara suna hade da kuma irin kudin da jihar ke samu a wancan lokaci daga gwamnatin tarayya da kuma duba da kudin da wadannan jihohin ke samu daga gwamnatin tarayya a wannan lokacin da muke ciki.
Koda shike ban yi bincike ba akan wannan amma ina da tabbacin tun rasuwarsa, kafin 1991 a shekarar da aka kirkiri jihar Kebbi zuwa kirkirar jihar Zamfara har kawo yanzu ba mu samu gwamnan da ya yi ayukka na cigaba ba irin wannan bawan Allah.
Shehu Kangiwa bai saci kudin gwamnati ba, hujja ta a nan shine idan ka dubi gidan da ya gina a lokacin rayuwarshi a cikin garin Argungu kuma a cikin wannan gidan kabarin shi yake, gida ne wanda bai kai ya kawo ba, gidan na nan hannun riga da babbar tashar mota a cikin garin na Argungu.
Sai mu yi duba da hankali da yadda wannan bawan Allah ya gudanar da ayukka a lokacin gwamnatinshi da kuma irin cigaban da aka samu a lokacin shi wanda har yanzu ana cin gajiyar ayukkanshi.
Muna fatar Allah ya jikanshi da rahama.
Daga Zaidu Bala ?ofa Sabuwa