Shekarar 2021: Majalisa Za Ta Yi Gyaran Kundin Tsarin Mulki

Majalisar wakilai za ta ba da kulawa ta musamman ga kokarin gyara kundin tsarin mulkin 1999 da aka yi wa kwaskwarima bayan dawowa daga hutun Kirsimeti da sabuwar shekara, kamar yadda jaridar The Nation rawaito.

Har ila yau, majalisar na tunanin ha?a hannu da ?angaren zartarwa gami da duk masu ruwa da tsaki a shirin sake duba kundin tsarin mulkin don tabbatar da kawo sauyi na gari.

Jaridar ta ce ta samu labarin cewa majalisar ta damu matu?a cewa gyaran da ake yiwa kundin tsarin mulki a baya ya gaza cimma nasarar da ake nema saboda haka ta kuduri aniyar tabbatar da cewa tsarin da za a yi yanzu bai zama irin wa?anda aka yi abaya ba.

Shugaban majalisar Femi Gbajabiamila ya ce za a hanzarta yin wa?annan sauye-sauye da zarar majalisa ta koma bakin aiki.

An da?e dai ana kiraye-kiraye ga ‘yan Majalisar dokokin tarayya da cewar su ?auki matakin yin gyara ko kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin ?asar, domin dacewa da bu?atun jama’ar Najeriya.

Related posts

Leave a Comment