Shekara Guda A Mulki: Jam’iyyun Siyasa Sun Yaba Buhari Sun Sokin Tsarin Tinubu

Muhammadu Buhari, President of the Federal Republic of Nigeria (cropped3)

Ƙungiyar gamayyar jam’iyyun siyasa (CUPP) ta kushe gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu cikin shekara daya da ya yi Kakakin kungiyar ya ce yan Najeriya sun sa ran samun sauki amma reshe ya juya da mujiya, wahala kawai suke sha ta kowanne fanni Har ila yau kakakin ya bayyana yadda tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fi Tinubu kokarin gudanar da mulki

Kungiyar gamayyar jam’iyyun siyasa (CUPP) ta caccaki gwamnatin shugaba Bola Tinubu kan rashin iya gudanar da mulki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kungiyar ta fitar da bayani kan gwamnatin Bola Tinubu ne domin auna kokarin da ya yi bayan shekara kan karaga

Kakakin kungiyar, Kwamared Mark Adebayo ne ya yi jawabin ga manema labarai a ranar Talata, 27 ga watan Mayu 2024.

Tsammanin ‘yan Najeriya ga Bola Tinubu Kungiyar CUPP ta ce yan Najeriya sun kyautata wa Tinubu zato kan cewa zai share musu hawaye amma sai ya kara jefa su cikin wahala. Yadda Tinubu ya rika tutiyar kwarewa da iya shugabanci an yi tsammanin samun haɓakar tattalin arziki, samun tsaro da cigaban ilimi amma hakan ya gagara.

Kungiyar CUPP ta ce ba ta yi tsammanin za a samu shugaba da zai yi kasa da abin da Muhammadu Buhari ya yi ba.

Amma sai ga shi cikin shekara daya Bola Tinubu ya kawo tsaruka da ya nuna yafi Muhammadu Buhari gazawa a kan gudanar da mulki.

Yadda Tinubu ya gasa talakawa Har ila ila yau kungiyar CUPP ta ce ba a taba samun shugaban da ya gasawa talakawa aya a hannu ba kamar Bola Tinubu. Ta ce abin bakin ciki ne a ce ranar da Tinubu ya karbi mulki talakawa suka fara dandana kudarsu a hannunsa saboda cire tallafin mai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply