Shekara ?aya Da Rasuwa: Abin Da Ba A Sani Ba Game Da Abba Kyari

An cika shekara ?aya da rasuwar shugaban ma’aikatan fadar shugaba Buhari, Malam Abba Kyari.

Abba Kyari ya rasu ne a ranar 17 ga watan Afrilun 2020 sakamakon rashin lafiya.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana marigayi Abba Kyari a matsayin babban amininsa na hakika kuma mai kishin kasa.

Buhari ya ce Abba Kyari amininsa ne tsawon shekaru 42 suna tare kafin daga baya ya zama shugaban ma’aikata a fadarsa.

Malam Abba Kyari ya rasu ne yana da shekara 67 a duniya bayan ya yi fama da cutar korona.

Related posts

Leave a Comment