Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

Sheikh Ɗahiru Bauchi Ya Amince Da Sanusi A Matsayin Halifan Tijjaniya

Babban malamin ɗarikar Tijjaniya a Tarayyar Najeriya, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya amince da tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi na II, a matsayin Khalifa.

Shehin malamin ya amince da naɗin Sunusi lokacin da tsohon sarkin na Kano ya gabatar masa da takaddar tabbatar da naɗinsa a hukumance a matsayin Khalifan darikar Tijjaniyya a Najeriya a ziyarar da ya kai jihar Bauchi, kamar yadda ɗaya daga cikin ƴaƴansa ya tabbatar wa BBC.

A makon da ya gabata aka kawo ƙarshen saɓani da ke tattare da naɗin tsohon Sarkin na Kano, Muhammadu Sanusi II, a matsayin jagoran Darikar Tijjaniyya a Najeriya a hedkwatar ɗarikar ta duniya dake ƙasar Senegal.

Babban jagoran darikar, Mahi Nyass ne ya tabbatar da naɗinsa lokacin da ya karbi bakuncin tsohon sarkin a wata ziyarar watan azumin Ramadan da ya kai ƙasar.

An ambato Sheikh Dahiru Bauchi na cewa naɗin na Sanusi bai rusa jagorancin sauran shugabannin darikar Tijjaniyya ba, musamman waɗanda marigayi Shiekh Ibrahim Nyas ya naɗa.

Shehin malamin ya yi wa tsohon sarkin na Kano addu’ar jagoranci da kariya ga matsayin da aka ba shi.

Sai yanzu aka naɗa sabon Khalifan Tijjaniya a Najeriya tun mutuwar marigayi Sheikh Isiyaka Rabiu a 2018.

Yanzu kuma Sanusi na II ya gaji kakansa Khalifan Tijjaniya na farko a Najeriya, wato Sarki Muhammadu Sanusi I

A watan Maris din 2021 a wani babban taron ɗariƙar da aka gudanar a jihar Sakkwato aka fara tabbatar da naɗin tsohon sarkin na Kano a matsayin jagoran ɗariƙar Tijjaniya a Najeriya.

Sai dai naɗinsa ya zo da ce-ce-ku-ce a Najeriyar inda wasu ɓangarorin Tijjaniyar suka ce ba su amince da naɗin nasa ba.

Amma yanzu amincewar da Shiekh Dahiru Bauchi ya yi da mabiyansa ya ƙara tabbatar da naɗin na Sanusi a matsayin Khalifan Tijjaniya a Najeriya

Rahoton BBC Hausa

Exit mobile version